logo

HAUSA

Sakatare janar na MDD ya yi tir da ci gaba da asarar rayuka da hare-haren Isra’ila ke haifarwa a Gaza

2024-08-13 12:03:48 CMG Hausa

 

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi tir da asarar rayuka da ake ci gaba da samu a zirin Gaza, biyo bayan mummunan harin da Isra’ila ta kai makarantar Al-Taba'een dake birnin Gaza a ranar Asabar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Palasdinawa sama da 100.

Cikin wata sanarwa, mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, ya ruwaito Antonio Guterres na yin tir da asarar rayuka a Gaza, ciki har da na mata da yara, yayin da Isra’ila ta kuma kai wani mummunan hari makarantar Al-Taba'een dake birnin Gaza, wadda ke zaman mafaka ga daruruwan Palasdinawa ‘yan gudun hijira da iyalansu. Haka kuma, ya ce harin ya haifar da jikkata da kara tsoro a zukatan jama’a da wahala da raba mutane da wajen zamansu.

Farhan Haq ya kara da cewa, sakatare janar din na maraba da kokarin shiga tsakani daga kasashen Amurka da Masar da Qatar, yana mai kira ga bangarorin masu rikici da juna da su sake shiga shawarwari, tare da kammala yarjejeniyar dakatar da bude wuta da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Majiyoyin tsaro da na kiwon lafiya a Palasdinu sun ce, sama da Palasdinawa 100 aka kashe yayin da wasu gommai suka jikkata sanadiyyar harin na Isra’ila kan makarantar Al-Taba'een dake yankin tsakiyar birnin Gaza, da safiyar ranar Asabar. (Fa’iza Mustapha)