logo

HAUSA

Adadin sufurin fasinjoji ta jiragen sama na Sin zai karu a shekarar 2024

2024-08-13 20:49:27 CMG Hausa

Shugaban hukumar lura da sufurin jiragen sama ta kasar Sin ko CAAC Song Zhiyong, ya ce a shekarar nan ta 2024, adadin sufurin fasinjoji ta jiragen sama na iya kaiwa miliyan 700.

Song Zhiyong, ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin bude taron yini 3 na tattauna batun tsaron sufurin sama na 2024, ko AP-SAS 2024, wanda aka bude a nan birnin Beijing.

Jami’in ya kara da cewa, sashen sufurin fasinjoji na kasar Sin, shi ne na biyu a duniya cikin shekaru 19 a jere, kuma gudummawar da yake bayarwa ga bunkasar sufurin sama na duniya ya zarce kaso 20 bisa dari.    (Saminu Alhassan)