logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Afirka na raya aikin noma na Afirka

2024-08-13 20:40:37 CMG Hausa

A cikin ’yan shekarun nan, an ci gaba da zurfafa hadin gwiwa a fannin aikin noma tsakanin Sin da Afirka, tare da samun sakamako mai inganci bisa wasu muhimman tsare-tsare. Tun daga gonaki har zuwa sayayyar intanet, kasar Sin tana taimaka wa kasashen Afirka inganta aikin noma, da inganta tsarin zamanantar da aikin noma a nahiyar Afirka, ta hanyar ba da taimakon fasaha, gina tsarin sana’o’i daban-daban, da fadada kasuwanni. A cikin shirinmu na yau, bari mu dubi yadda kasar Sin ke yin hadin gwiwa da Afirka a fannin aikin noma, tare da tsara salon raya aikin noma na Afirka tare da jama'ar Afirka.