logo

HAUSA

PBIC: Matasa sun samar da sabbin daftarin kara kyan Afirka

2024-08-13 07:27:44 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, a kwanan baya, an gama gasar yin kirkire-kirkire kan harkokin tallafawa jama’a ta matasan kasa da kasa ta PBIC karo na 8, wato bikin nuna shirye-shiryen tallafawa jama’a na Afirka da matasan suka yi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Cikin gasa din mai tsawon watanni biyu, matasan kasar Sin sun gabatar da sabbin ra’ayoyi game da yadda za a warware matsaloli masu nasaba da zamantakewar al’umma a kasashen Afirka.