logo

HAUSA

Mutane 68 ne suka mutu sakamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa a Sudan

2024-08-13 10:57:09 CMG Hausa

Ministan harkokin cikin gida na kasar Sudan Khalil Pasha Sairin ya bayyana jiya Litinin cewa, kimanin mutane 68 ne suka mutu sakamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa da ta afkawa wasu sassan Sudan tun daga wata Yuni.

Sanarwar da ministan ya fitar ta ce, adadin mutanen da suka mutu sakamakon mabambantan dalilai na ambaliyar ruwa da ruwan sama cikin har da rushewar gidaje da nutsewa ya kai 68, yayin da mutane 130 suka samu raunuka.

Fiye da gidaje 4,000 ne suka ruguje gaba daya, kuma gidaje 8,000 sun dan rushe, sannan wasu gine-gine 40 na gwamnati da masu zaman kansu sun lalace, yayin da kimanin murabba'in kilomita 832 na filayen noma suka lalace, kuma wasu dabbobi suka mutu.

Ambaliyar ruwa, wacce ke faruwa kowace shekara a Sudan, yawanci tana faruwa ne tsakanin Yuni da Oktoba. A cikin shekaru uku da suka gabata, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane tare da lalata filayen noma. (Mohamed Yahaya)