logo

HAUSA

Shugaba Tinubu ya kaddamar da motocin bas masu amfani da iskar gas na CNG a birnin Abuja

2024-08-13 09:49:32 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da motocin bas guda 30 masu amfani da makamashin gas na CNG a birnin Abuja.

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa ce ta bayar da gudummawar motocin wanda aka kaddamar a fadar shugaba kasa jiya Litinin 12 ga wata.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Bikin kaddamar da motocin wanda aka gudanar jim kadan bayan kammala taron majalissar zartarwa ta kasa.

A jawabinsa yayin kaddamar da motocin, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada bukatar Najeriya da ta alkinta albarkatun gas da take da shi a bangaren harkokin sufuri.

Ya ce, sauyawa wajen amfani da makamashin gas na CNG wajen sufuri abu ne da ya zama wajibi ga ’yan Najeriya ta fuskar tattalin arzikinsu.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ci gaba da bayanin cewa, fara amfani da makamashin CNG wajen sufuri a Najeriya babu shakka dai zai kasance mafita ga tsadar sufuri da ’yan kasa ke fuskanta da dadewa, inda ya ce, irin wannan mataki kasashe kamar Indiya suka dauka tun a 2004.

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce, motocin sufuri na ’yan kasuwa su ne suke amfani da kaso 80 na man fetur da gwamnati ke sayowa na biliyoyin naira a duk wata, a saboda haka yanzu mun samo wata hanya mafi sauki gare mu, kuma za mu ci gaba da aiki da ita domin samar da makoma ta-gari ga ’yan Najeriya.

“Ina bayyana farin cikin karbar wadannan motocin bas a madadin gwamnati, wanda wannan wani muhimmin ci gaba ne ta fuskar kirkire-kirkire a fagen sha’anin sufuri.”

Kowace motar bas dai za ta iya daukar adadin fasinsojji 100 a lokaci guda, kuma za a iya amfani da man dizal idan ana bukata baya ga makamashin CNG. (Garba Abdullahi Bagwai)