Kasar Sin: Dawwamammen ci gaba shi ne tushen zaman lafiya mai dorewa a Afrika
2024-08-13 10:15:28 CMG Hausa
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce abu mafi muhimmanci wajen shawo kan rashin adalcin da aka dade ana yi wa nahiyar Afrika shi ne, mara baya ga kasashen nahiyar a kan tafarkin samun dawwamammen ci gaba, a matsayin tushen samun zaman lafiya mai dorewa.
Fu Cong, ya bayyana haka ne a jiya Litinin, yayin wata muhawara ta Kwamitin Sulhu na MDD kan “shawo kan rashin adalcin da aka dade ana yi wa nahiyar Afrika”, inda ya ce, nahiyar ta riga ta nunawa duniya karfinta.
Ya kara da cewa, domin gano bakin zaren rashin adalcin da ake yi wa nahiyar, dole ne kasa da kasa su yi adawa da ra’ayin mulkin mallaka da dukkan wasu ayyukan babakere. Haka kuma, ya kamata kasashen yamma su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu yadda ya kamata, su sauya alkibla, tare da dakatar da dukkan abubuwa marasa dacewa na tsoma baki da matsin lamba ta hanyar kakaba takunkumai da mayar da makomar Afrika hannu mutanen Afrika.
A nasa bangare, sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a inganta wakilcin nahiyar Afirka a kwamitin sulhu na majalisar domin tabbatar da cikakken halacci da sahihancin kwamitin.
Ya kara da cewa, duniya ta sauya, amma tsarin wakilci a kwamitin ba ya tafiya tare da zamani. Ya ce, ba za a amince da ganin hukumar tabbatar da tsaro da zaman lafiya ta duniya mafi muhimmanci a duniya ba ta da kujera ta dindindin ga nahiyar dake da mutane sama da biliyan 1, adadin da ya dauki kaso 28 na mambobin MDD. (Fa’iza Mustapha)