Atisayen hadin gwiwar sojojin Sin da na Tanzania ya shiga matakin karshe
2024-08-12 19:01:24 CMG Hausa
A jiya Lahadi ne sojojin kasar Sin da na Tanzania, suka gudanar da atisayen hadin gwiwa na yaki da ta’addanci, a babbar cibiyar samar da horo dake Tanzania. Bayan shafe kusan sa’o’i 2, sojojin sun kammala atisayen, an kuma bayyana cewa, atisayen mai lakabin "Wanzar da zaman lafiya da hadin kai a 2024" ya shiga matakin karshe.
Mashirya atisayen, sun ce yayin da sojojin ke gudanar da shi, sun mayar da hankali ga dabarun yaki da ayyukan ta’addanci, masu kunshe da cikakkun tsare tsare da dabarun yaki, da nuna ikon sauke nauyin wanzar da zaman lafiya.
An kuma ce sojojin kasa na Sin da suka shiga atisayen, za su fara komawa gida cikin rukunoni daban daban, tun daga gobe Talata 13 ga watan Agustan nan, ta amfani da jiragen sama da na ruwa. (Saminu Alhassan)