logo

HAUSA

Linda Painan: Taimakawa baki don rungumar rayuwa a birnin Shanghai

2024-08-12 14:16:34 CMG Hausa


Linda Painan, 'yar kasar Singapore, ta shafe shekaru 27 tana zama a Shanghai. Ta lashe lambar yabo ta azurfa ta furen Magnolia ta Shanghai ta shekarar 2023. Gwamnatin birnin Shanghai ce ta kaddamar da wannan lambar yabon, wadda aka sanya wa sunan furen birnin wato furen Magnolia a shekarar 1989, domin karrama fitattun baki 'yan kasashen waje saboda kyakkyawar gudummawar da suka bayar wajen yin cudanyar kasa da kasa da birnin Shanghai. Painan uwa ce mai 'ya'ya uku, 'yar kasuwa, kuma mai fafutukar kare hakkin jama'a da jin kai a cikin al'ummar kasa da kasa ta Shanghai.

Painan ita ce shugabar cibiyar Baki ta TEC a karkashin Cibiyar Hidimar Rayuwa ta Iyali ta Shanghai, kuma ita ce mataimakiyar shugabar kungiyar kawance ta Hongqiao a yankin Changning ta Shanghai.

TEC wani muhimmin aiki ne na Cibiyar Hidimar Rayuwar Iyali ta Shanghai. Manufarta ita ce a taimaka wa ‘yan kasashen waje wajen kyautata zaman rayuwa a kasar waje. Tare da goyon bayan gwamnatin yankin Changning da ofishin reshen Hongqiao na yankin, Painan ta kafa wani dandali na hadin gwiwa tsakanin gwamnati da jama'a, da aikin ba da hidima kai tsaye don taimakawa 'yan kasashen waje da Sinawa da suka dawo daga kasashen waje su kara cudanya da zaman gida.

Painan ma'aikaciyar Bankin Deutsche ce a lokacin da ta fara ziyartar Shanghai, kuma an tura ta birnin don bin diddigin wani aiki ne. Painan ta bayyana cewa, "bayan na zauna a birnin Shanghai na wani dan lokaci, na gano cewa birnin Shanghai, a matsayin cibiyar tattalin arziki mafi girma a kasar Sin, kuma babban birni ne na kasa da kasa, yana da fa'ida ta musamman wajen samun ci gaba. Yadda birnin yake da kuzari, da mabambantan ra'ayoyi da kuma karfin ci gabansa ya burge ni kwarai da gaske, ganin cewa magabatana Sinawa ne. Na yi tunani, a wancan lokacin, cewar ‘Mu dawo nan’."

A shekarar 1997, Painan da mijinta sun koma Shanghai, inda suka tsunduma cikin harkokin kasuwanci. Daga baya, Painan ta fara shiga ayyukan agaji da jin dadin jama’a.

Lokacin da aka tambaye ta yadda ta yanke shawarar kirkirar ayyukan ba da tallafi da ke taimaka wa ‘yan kasashen waje, Painan ta tuna ‘yar kasar waje ta farko da ta taimakawa. A wurin gyaran farce ne, inda ta ci karo da wata Ba’Amurkiya da ke fuskantar matsalar magana da ma’aikata Sinawa. Ganin yadda matar ke cikin damuwa, Painan ta ba da taimako.

Matar ta gaya wa Painan matsalolin da take fuskanta wajen daidaita rayuwa a Shanghai. Mijin matar shi ne babban manajan ofishin wani kamfanin Amurka da ke birnin Shanghai. Bambancin al'adu da yare sun saka ta cikin damuwa da kadaici. Ta bayyana cewa ta shirya komawa Amurka tare da danta mai shekaru 4 a wannan daren.

Painan ta karfafa wa matar gwiwa da ta sake ba Shanghai wata damar, kuma ta jaddada mahimmancin kasancewar iyali tare a wuri guda. A cikin kwanakin da suka biyo baya, Painan ta raka matar zuwa yawo tare da kara fahimtar rayuwa a Shanghai, kuma ta taimaka wa matar da aikin tafinta da sadarwa. Painan ta kuma ba da haske game da abubuwan al'adu na birnin.

Sun ziyarci Dongjiadu, inda ake iya samun yadudduka daban-daban da teloli masu yawa. Matar, wacce take sha’awar tsara fasalin adiko, da zanin shimfida, ta sayi yadudduka, ta kuma nemi tela da ya dinka mata zannuwan shimfida, bisa la’akari da yadda ta tsara.

Ganin hazakar matar, Painan ta ba da shawarar cewa za ta iya sayar da kayayyakin a baje kolin makarantu na kasa da kasa, sannan ta ba da kudaden da aka samu ga mabukata. Painan ta ce, "ta wannan hanyar, rayuwarta a Shanghai ta kasance cikin wadata, kuma mai ma'ana. Na taimaka mata, kuma na kai ta wurin da za ta yi aikin agaji da jin dadin jama’a, wanda kuma yana da ma'ana."

Yayin da take taimakawa matar, Painan ta fahimci cewa dole yawancin baki su dan shiga rudani lokacin da suka fara isowa kasar Sin. Duk da cewa suna rayuwa mai kyau, suna fuskantar matsaloli da yawa a rayuwarsu ta yau da kullun, musamman a bangaren bambancin al'adu. Don haka, Painan ta yanke shawarar, suna bukatar jagorancin kwararru da mafita wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.  

A shekarar 2014, Painan ta sa kai a ayyukan Cibiyar Hidimar Rayuwa ta Iyali ta Shanghai. A shekarar 2018, ta kafa TEC, tare da manufar taimaka wa baki sajewa da rayuwar wurin, da kuma jin dadin zama a Shanghai.

Painan ta ce, “a matsayina na wadda ta samu lambar yabo ta azurfa ta furen Magnolia ta Shanghai ta shekarar 2023, Karrama ni da aka yi ba wai kawai don shekarun da na yi na hidimar al'umma ba ne, har ma da nuna irin gudunmawar da al'ummar baki ke bayarwa, wadda tawagar TEC da nake jagoranta ta wakilta, wajen ba da gudummawa ga ci gaba da wadatar birnin."

A karkashin jagorancin Painan, TEC ta shirya baje kolin kasa da kasa na 3E wato Kasuwanci, Samar da Aiki, da Masana’anta na tsawon shekaru hudu a jere tun daga shekarar 2020. Baje kolin ya kasance wani dandalin da ya hada kan kamfanoni na kasa da kasa da na cikin gida a birnin Shanghai, don samar da guraben ayyukan yi ga dubban mutane.  (Kande Gao)