logo

HAUSA

Hamas ta yi kira da a aiwatar da shawarwari da aka yi a baya kan tsagaita wuta a Gaza

2024-08-12 11:38:48 CMG Hausa

 

Kungiyar Hamas a cikin wata sanarwar da ta fitar a jiya Lahadi, ta yi kira ga masu shiga tsakani na tsagaita bude wuta a zirin Gaza da su gabatar da wani shiri na aiwatar da shawarwari da aka amince a baya maimakon zuwa wani sabon zaman tattaunawa ko gabatar da sabbin shawarwari.

Kungiyar ta kara da cewa, tun farkon rikicin Gaza, kungiyar Hamas ta himmatu wajen ganin cewa masu shiga tsakani a Masar da Qatar sun yi nasara wajen cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen yakin da ake yi da al'ummar Gaza, ta kuma tabbatar da goyon bayanta ga duk wani yunkuri na ganin an dakatar da yakin.

Sanarwar ta kara da cewa, ko da yake Hamas da masu shiga tsakani suna sane da hakikanin aniya da matsayar Isra'ila, kungiyar ta mayar da martani ga yarjejeniyar karshe a farkon watan Yuli, amma Isra'ila ta tunkareta da wasu sabbin sharuddan da ba a gabatar da su ba a duk lokatun da ake gudanar da shawarwari ba, sannan kuma ta ci gaba da zafafa yakin da take yi.  

Bisa la'akari da haka, da nuna damuwa da kuma yin abin da ya dace ga al'ummar Gaza da muradunsu, kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da su gabatar da wani shiri na aiwatar da abin da suka gabatar wa kungiyar a baya da kuma wajibtawa Isra'ila yin hakan. (Yahaya)