logo

HAUSA

Me ya sa Sin ta jawo hankalin sassan kasa da kasa yayin gasar wasannin Olympics ta Paris

2024-08-12 19:48:39 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne aka kammala gasar wasannin Olympics ta Paris ta 2024 bayan kwashe kwanaki 19 ana gudanar da ita. Tawagar Sin ta samu lambobin yabo na zinari guda 40, da lambobin yabo na azurfa guda 27, da kuma lambobin yabo na tagulla guda 24, ta kuma samu sakamako mafi kyau a tarihin ta na shiga gasar wasannin Olympics ta yanayin zafi a kasashen waje.

Yayin wata hira da dan jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG a kwanan baya, shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bayyana cewa, daga wasan kwallon tebur zuwa wasan ninkaya da sauran wasanni, tawagar Sin ta samu sakamako mai kyau, wanda ya shaida kwarewar kasar Sin a fannin horar da ‘yan wasa masu hazaka, kuma ta kware wajen karfafa gwiwar al’ummun ta.

Tun bayan da tawagar Sin ta samu lambar yabo ta zinari ta farko a shekarar 1984, zuwa lokacin da tawagar Sin din ta kasance a matsayin farko wajen lashe jerin lambobin zinari a gasar wasannin Olympics ta 2024, a cikin shekaru 40, gasar wasannin Olympics ta shaida yadda Sin ta samu ci gaba a wasannin motsa jiki na takara, da kara karfin ta, da kuma ba da muhimmiyar gudummawa ga ci gaban wasannin motsa jiki na Olympics. (Safiyah Ma)