Wakiliyar musamman ta shugaba Xi Jinping ta halarci bikin rufe gasar Olympics
2024-08-12 14:54:27 CMG Hausa
An rufe gasar wasannin Olympics na lokacin zafi karo na 33 a birnin Paris na kasar Faransa a jiya 11 ga wata, kuma madam Shen Yiqin, wakiliyar musamman ta shugaban kasar Sin Xi Jinping ta halarci bikin.
Kafin a fara bikin, madam Shen Yiqin ta tattauna tare da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da ma mai dakinsa Brigitte Macron, wadanda suka taya ’yan wasan kasar Sin murnar gaggaruman nasarorin da suka cimma, tare da bayyana godiyarsu ga gwamnatin kasar Sin bisa goyon bayan da ta samar wa Faransa wajen gudanar da wasannin Olympics a Paris.
A ranar 10 ga wata kuma, madam Shen Yiqin ta gana da shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, Thomas Bach, inda ta bayyana cewa, kasar Sin na son ganin ta zurfafa hadin gwiwa tare da kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, don samar da karin gudummawa wajen raya wasannin Olympics da kuma gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama. Mr. Bach a nasa bangaren ya bayyana godiya ga gwamnatin kasar Sin kan goyon bayan da ta nuna wa wasannin Olympics, yana kuma fatan inganta hadin gwiwa tare da kasar. Bangarorin biyu sun kuma bayyana ra’ayinsu na bai daya na rashin amincewa da siyasantar da wasannin. (Lubabatu Lei)