Firaministar Congo Kinshasa: Cibiyar al’adu ta tsakiyar Afirka ta kara shaida nasarar hadin gwiwar kasar da kasar Sin
2024-08-12 14:02:26 CMG Hausa
Firaministar jamhuriyar dimokuradiyyar Congo Judith Tuluka Suminwa ta bayyana a kwanan baya a birnin Kinshasa, babban birnin kasar cewa, cibiyar al’adu da fasaha ta tsakiyar Afirka da ke Kinshasa da gwamnatin kasar Sin ta ba da gudummawar ginawa ta kasance wani karin misali da ya shaida nasarar hadin gwiwar kasashen biyu.
Madam Tuluka ta jagoranci ministoci da dama zuwa inda ake gina cibiyar, inda ta bayyana gamsuwarta game da yadda ake gudanar da aikin, da ma yakininta game da muhimmiyar rawar da cibiyar za ta taka ta fannin musayar al’adu tsakanin Afirka da Sin.
Jakadan kasar Sin a Congo Kinshasa din, Mr. Zhao Bin ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na son hada gwiwa da kasar Congo Kinshasa, don sa kaimi ga musayar wayewar kai tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma karfafa fahimtar juna da dankon zumunci a tsakanin al’ummar sassan biyu.
Cibiyar dai na kunshe da wani babban gidan wasan kwaikwayo da ke iya daukar mutane 2000, da wani karamin gidan wasan kwaikwayo da ke iya daukar mutane 800, baya ga harabar kwalejin nazarin fasaha na kasar da ke iya daukar dalibai 2000. (Lubabatu Lei)