logo

HAUSA

Belarus: An gano sassan da kasashen NATO suka hada a cikin tarkacen jiragen sama maras matuki na Ukraine

2024-08-11 15:05:20 CMG Hausa

A jiya Asabar, gidan talabijin na kasar Belarus ya nuna hotunan tarkacen jiragen sama marasa matuka na kasar Ukraine, wadanda aka harbo bayan kutsawarsu cikin sararin samaniyar Belarus a ranar Juma’a. A cewar gidan talabijin din, tarkacen jiragen na kunshe da sassan da kasashen kungiyar tsaro ta NATO suka hada.

Kafin hakan, shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko, ya bayyana cewa sojojin kasar Ukraine sun keta ka'idojin kasa da kasa, ta hanyar kutsawa sararin samaniyar Jamhuriyar Belarus.

Da karfe 6 na maraicen ranar Juma’a bisa agogon Belarus, rundunar sojan sama, da sojojin tsaron sararin samaniya na Belarus, sun shiga damarar dauki-ba-dadi a matsayin farko. Daga bisani ne kuma suka harbo wasu jiragen sama da dama da suka keta sararin samaniyar kasar.

Belarus na zargin kasar Ukraine da kaddamar da matakin kutse ta  jiragen saman yaki marasa matuka, wadanda suka tashi daga harabar kasar ta Ukraine. (Bello Wang)