Kungiyar kasar Sin ta lashe lambar zinare a gasar kwallon tebur ta kungiyoyin mata a gasar Olympics ta Paris
2024-08-11 15:03:53 CMG Hausa
A jiya Asabar, a wasan karshe na gasar kwallon tebur na kungiyoyin mata na gasar Olympics dake gudana a birnin Paris na kasar Faransa, kungiyar kasar Sin da ta kunshi Chen Meng, da Sun Yingsha, da Wang Manyu, sun doke tawagar kasar Japan tare da lashe lambar zinare. Wannan shi ne karo na biyar a jere, da tawagar kasar Sin ta zama zakara a gasar kwallon tebur ta kungiyoyin mata yayin gasar wasannin Olympics, kuma karo na farko da tawagar kasar Sin ta samu dukkan lambobin zinare guda biyar a gasar wasan kwallon tebur ta Olympics.
Ban da haka, an ce, wannan lambar zinare ita ce cikon ta 37 da tawagar 'yan wasan kasar Sin ta samu, a gasar Olympics ta Paris, kuma ta 300 da tawagar 'yan wasan kasar Sin ta samu a tarihinta na halartar gasar Olympics ta lokacin zafi. (Bello Wang)