Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kamaru FECAFOOT Samuel Eto’o ya kai wata ziyara aiki a Niamey
2024-08-11 14:51:20 CMG Hausa
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasar Kamaru, Samuel Eto’o ya samu ganawa da shugaban kwamitin ceton kasa CNSP, birgadiye janar Abdourahamane Tiani a ranar jiya Asabar 10 ga watan Augustan shekarar 2024 a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
A karshen wannan ganawa, tsofon kaftin din kungiyar ‘yan wasan Les lions Indomptabales na Kamaru ya bayyana yabonsa ga kungiyar kwallon kafa ta kasar Nijar FENIFOOT, ga shugabanta kanal Djibilla Hima Hamidou da kuma daukacin al’ummar Nijar.