SAF ta yi ikirarin dakile hare haren RSF a birnin El Fasher
2024-08-11 16:05:18 CMG Hausa
Rundunar sojojin kasar Sudan ko SAF, ta ce ta yi nasarar dakile wasu hare hare da dakarun daukin gaggawa na kasar ko RSF suka kaddamar jiya Asabar a birnin El Fasher, fadar mulkin jihar North Darfur ta shiyyar yammacin kasar.
Da yake tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, kakakin rundunar ta SAF Nabil Abdallah, ya ce dakarun sojin gwamnati sun murkushe babban harin mayakan RSF tare da fatattakar su.
Ita ma a nata bangaren, hadakar dakarun gwagwarmaya a yankin Darfur, mai alaka da sojojin gwamnatin kasar, ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, yayin dauki ba dadin da aka yi a El Fasher a jiya, dakarun RSF sun gamu da mummunar asara.
Kaza lika, wakilcin gungun kwamitocin gwagwarmaya na al’ummun Sudan a El Fasher, ya ce an tsagaita fada a birnin bayan dauki ba dadi na sama da sa’o’i 6. To sai dai duk da hakan, cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na Facebook, ofishin tsare tsare na kwamitocin, ya ce duk da an tsagaita wuta, dakarun RSF sun ci gaba da harba makaman atilari zuwa kasuwanni, da asibitoci, da gidajen fararen hula, lamarin da ya haifar da jikkatar mutane da dama.
Kawo yanzu dai rundunar ta RSF ba ta bayyana matsayar ta kan wannan batu ba. (Saminu Alhassan)