An kai hari kan wata makaranta a zirin Gaza
2024-08-10 17:17:47 CMG Hausa
Ofishin watsa labaru na kungiyar Hamas ta Palesdinu ya bayar da sanarwa a yau cewa, sojojin kasar Isra’ila sun kai hari kan wata makaranta a zirin Gaza, wanda ya haddasa mutuwar mutane fiye da 100, yayin da goman mutane suka jikkata.
Sanarwar ta bayyana cewa, akwai mutane da dama da suka rasa gidajensu a cikin makarantar Al-Taba'een, wasu suna cikin addu’a yayin da sojojin Isra’ila suka kai harin. Saboda yawan mutanen da suka mutu a sakamakon harin, masu ba da ceto ba su gano dukkan gawawwakin mutanen da suka rasu ba. Sanarwar ta ce, kungiyar Hamas ta yi Allah wadai da wannan hari.
Sojojin tsaron Isra’ila sun bayar da sanarwa a wannan rana cewa, sojojin saman kasar sun kai hari kan wata cibiyar ba da umurni ta kungiyar Hamas dake makarantar Al-Taba'een, wadda ke dab da masallaci a zirin Gaza. Bangaren Isra’ila ya ce, wannan na daya daga cikin wuraren zaman membobin kungiyar Hamas. (Zainab Zhang)