Sin ta ki amincewa da duk wanda ya yi amfani da gasar Olympics wajen yada yunkurin ‘yan aware na yankin Taiwan
2024-08-10 17:10:37 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a jiya cewa, Sin tana fatan bangarori daban daban za su bi ka’idojin kundin tsarin mulkin Olympics, da girmama da kiyaye gudanarwa da wasanni ba tare da wata boyayyar manufa ba. Sin na adawa da duk wanda ya yi amfani da gasar wasannin Olympics wajen yada yunkurin ‘yan aware na yankin Taiwan, da kawo matsala ga gudanar da gasar yadda ya kamata.
Akwai tambayar cewa, mene ne ra’ayin Sin kan batun wani dan kallon gasar wasannin Olympics ta Paris da ya daga takardar dauke da rubutun “Kara kuzari, Taiwan”, duk da cewa an janye takardar a wurin. Game da wannan batu, Mao Ning ta yi nuni da cewa, kasar Sin daya tak ce a duniya, yankin Taiwan yanki ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi daga Sin ba. Game da tawagar Chinese Taipei da ta halarci gasar wasannin Olympics a wannan karo, kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa wato IOC ya riga ya tsai da ka’idoji kan batun bisa ka’idar Sin daya tak a duniya, bangaren wasanni na kasa da kasa sun mutunta ka’idojin. Kana bisa kundin tsarin mulkin Olympics, an riga an tsai da ka’idoji game da yada yunkurin siyasa a dakunan wasannin Olympics. (Zainab Zhang)