logo

HAUSA

Kasar Sin ta lashe karin lambobin zinari a rana ta 14 ta gasar Olympics ta Paris

2024-08-10 16:43:52 CMG Hausa

 

A ranar Juma’a 9 ga watan Agusta ne dan wasan kasar Sin Ma Long ya zama dan wasan Olympics da ya fi kowa yawan kambi a kasar, inda ya lashe lambar zinari ta shida tare da takwarorinsa Wang Chuqin da Fan Zhendong, yayin da suka doke kasar Sweden a wasan kallon tebur.

Kazalika, Xu Shixiao da Sun Mengya su ma sun lashe lambar zinari ga kasar Sin a gasar kwale-kwale ta mita 500 ta mata a filin wasa na Vaires-sur-Marne Nautical.

Haka kuma Chen Yiwen ta lashe lambar zinari a gasar nutso ko Springbord mita 3 ta mata, wanda ya kara yawan nasarar da kasar Sin ta samu a wasannin nutso na gasar wasannin Olympics ta shekarar 2024 zuwa bakwai. Kuma ita ce kadai ‘yar wasan nutso a ranar Juma'a da ta samu maki sama da 70 a kowane zagaye.

Har ila yau, 'yar wasan kasar Sin Wu Yu ta yi nasarar lashe lambar zinari a gasar dambe ta mata mai nauyin kilogiram 50. (Yahaya)