logo

HAUSA

Gasar Olympic ta Paris 2024: wasan takobi zai kayatar

2024-07-26 15:14:03 CMG Hausa

Yayin da hankula ke kara karkata ga gasar Olympic ta birnin Paris ta shekarar nan ta 2024 wadda za a bude a karshen makon gobe, masharhanta harkokin wasanni na cewa gasar fadan takobi ko “fencing” za ta kayatar matuka. A wannan karo dai gasar ta Olympic za ta gudana ne a tsohon birnin Paris na Faransa, wanda ake sa ran zai samar da kyakkyawar tarba ga ‘yan wasa da masu sha’awar kallon wasanni.

Kasar da za ta karbi bakuncin gasar wato Faransa, da Italiya, sun jima suna mamaye nasarar wasan “fencing”, kuma a gasar dake tafe ma ana hasashen ba bu abun da zai sauya, musamman ganin cewa kasashe biyu ne kadai suka gabatar da rajistar cikakkun ‘yan wasan “fencing” ga kwamitin shirya gasar Olympic ta kasa ko NOC, inda suka gabatar da ‘yan wasa 18, da suka hada da maza 9 mata 9.

Albarkacin goyon bayan masu mara baya na gida, ana sa ran Faransa za ta nuna bajimta a dukkanin wasannin fasahar sarrafa makamai a gasar, inda za ta baje kolin kwararru, kuma tsofaffin ‘yan wasa da kuma masu tasowa, ciki har da dan wasan kasar da ya lashe lambar zinari a gasar Olympic ta Tokyo ta shekarar 2020 wato Romain Cannone, da zakaran wasan na duniya Yannick Borel, wanda ake ganin ya kware sosai wajen nuna fasahohin wasan na “fencing”. A daya bangaren kuma, ‘yar wasan kasar da ta lashe kambin duniya har sau 6, Manon Apithy-Brunet ita ma ana sa ran ganin za ta nuna bajimta, tare da lashe lambar yabo, sama da lambar tagulla ta “sabre” da ta samu a gasar Tokyo.

A bangaren kasar Italiya kuwa, wadda ke rike da kambin lashe mafi yawan lambobin yabo a wasan na “fencing”, ana sa ran a wannan karo za ta farfado sosai, bayan rashin nasara da ta ci karo da shi a gasar Tokyo, inda a gasar ta Tokyo ta lashe lambobin azurfa kwaya biyu da tagulla 3 kacal. Dan wasan “fencing” na kasar wanda ya lashe lambar zinari ta gasar Olympic ta birnin Rio a shekarar 2016 Daniele Garozzo, da kuma dan wasan kasar mai rike da kambin mafi kwarewa a duniya Tommaso Marini, dukkanin su za su fafata domin neman lashe lambar zinari a gasar ta Paris ajin maza.

A bangaren mata kuwa, ‘yan wasan na “fencing” masu rike da kambin duniya Arianna Errigo, da Alice Volpi, da kuma tauraruwar wasan mai shekaru 22 Martina Favaretto, dukkanin su za su fafata neman lashe lambar kwarewa karkashin tawagar kasar ta Italiya.

A baya, babbar abokiyar hamayyar Italiya a wasan na fadan takobi ko  “fencing” ita ce kasar Amurka. ‘Yar wasan Amurka Lee Kiefer ta zamo ‘yar wasan kasar ta farko da ta taba lashe lambar zinari a gasar “fencing” ta Olympic a birnin Tokyo, bayan nasarar da takwararta daga Rasha Inna Deriglazova ya samu a gasar. A daya bangaren kuma, mai gidan Lee Kiefer wato Gerek Meinhardt, wanda shi ma tauraron wasan na “fencing”ne, zai yi fitowa ta 5 a gasar Olympic, bayan da ya lashe lambobin tagulla 2 a gasannin shekarun 2016 da 2021.

Ita ma kasar Hungary na da ‘yan wasan “fencing” masu kwarewa, ciki har da tauraron wasan Aron Szilagyi, wanda a gasar Olympic ta London, da Rio, da Tokyo ya lashe lambobin zinari 3 a jere. A halin yanzu shi ne ke a matsayi na 5 a duniya. Szilagyi mai shekaru 34 a duniya ya yi nasara ne sau daya a gasar fadan takobin ta duniya a kakar bana. To sai babbar tambaya ita ce, ko zai iya ci gaba da haskakawa a wannan karo da zai shiga gasar Olympic a karo na 5 ko a’a.

Wani abun lura ma shi ne yadda ake sa ran dan wasan “fencing” daga Koriya ta kudu Sang-uk zai haskaka, har ma wasu ke ganin zai iya zamewa Szilagyi babban kalubale wajen kare kambinsa. Sang-uk ya kware a wasan “fencing” ajin “sabre”, inda a baya ya lashe lambobin zinari 2 a ajin maza na gasannin Olympic na biranen London da Tokyo. Har ila yau, daga koriya ta kudun akwai kwararren dan wasan ta Gu Bon-gil, mai rike da lambar karramawa ta duniya, da kuma lambar yabo ta nahiyar Asiya, wanda shi ma ake ganin zai yi wa koriya ta kudun kyakkyawan wakilci.

Baya ga kasashe masu kwararrun ‘yan wasa, a gefe guda kuma kasashe irin su Sin, da Japan, da Ukraine, da Masar da Estonia, su ma za su gabatar da ‘yan wasa masu kwazo a wasan. Cikin ‘yan wasan da ake fatan za su taka rawar gani akwai Sun Yiwen daga kasar Sin, da Vivian Kong, Man Wai da Cheung Ka Long daga yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, sai kuma Misaki Emura, da Koki Kano daga Japan, da Olga Kharlan daga Ukraine.

Ana sa ran gudanar da wasannin “fencing” a gasar ta Olympic tun daga 27 ga watan Yulin nan zuwa 4 ga watan Agusta, inda ‘yan wasa maza da mata za su fafata a ajin wasan na “sabre” da “epee” a fafatawar daidaikun ‘yan wasa da kuma na tawagogi.

Paris 2024: Ana sa ran Sin za ta yi rawar gani a wasan tsunduma cikin ruwa ko “Diving”

A matsayin ta na kasa dake da manyan ‘yan wasan tsunduma cikin ruwa ko “Diving”, kasar Sin ta ci gaba da kare kambin ta na lashe lambobin zinari a wasan, kuma haka ake sa ran gani a yayin gasar Olympic ta birnin Paris dake tafe nan da ‘yan kwanaki.

Tun daga gasar Olympic ta 1984 da aka yi a birnin Los Angeles, tawagar "Dream Team" ta Sin ta ci gaba da nuna bajimta, inda kawo yanzu ta samarwa kasar Sin jimillar lambonin zinari 47 a gasannin Olympic. To sai dai kuma duk da tsayin lokaci da ‘yan wasan tawagar suka kwashe suna cimma nasarori, har yanzu ba su kai ga yin nasarar lashe dukkanin lambobin yabo a gasar Olympic ba, wato dai kusan ko wane lokaci wasu daga lambobin suna kubucewa kungiyar. A gasannin Olympic biyu da suka gabata, a fannin wannan wasa na “Diving”, kasar Sin ce ke da 7 daga cikin lambobin zinari 8 da aka fafata a kan su.

Cinkin ‘yan wasan da za su wakilci kasar Sin a gasar ta Olympics dake tafe a Paris, akwai ‘yan wasan kasar 5 wadanda a baya suka taba lashe lambobin zinari a gasar Olympic a wasan na “Diving”, da suka hada da Cao Yuan wanda, wanda a wannan karo zai shiga gasar a karo na 4. Sai kuma Quan Hongchan, da Chen Yuxi, da Wang Zongyuan, da Xie Siyi wadanda a wannan lokacin ne za su shiga gasar ta Olympic a karo na 2. Sai kuma Chen Yiwen, da Chang Yani, da Long Daoyi, da Yang Hao, da Lian Junjie wadanda za su shiga gasar a karon farko.

Wani abun lura a nan shi ne, mai yiwuwa damar farko ta kasar Sin ta lashe lambar zinari a gasar Olympic na Paris ta wannan wasa na “Diving”, za ta zo ne daga ‘yan wasan kasar ajin mata, wadanda za su fafata a ajin ‘yan wasa masu yin tsalle-tare, da kuma tsunduma cikin ruwa daga tudun mita 3, wanda za a fara gudanarwa tun daga ranar 27 ga watan nan na Yuli.