IOM ta taimakawa bakin haure 292 komawa Najeriya da Mali
2024-08-09 10:02:38 CMG Hausa
Hukumar kula da 'yan ci rani ta kasa da kasa IOM, ta ce ta taimakawa bakin haure 292 komawa kasashen su na asali daga Libya.
Sanarwar da hukumar ta fitar a jiya Alhamis, ta ce a ranar Talata jirgin farko dauke da bakin haure 163 daga yankunan Brak Alshati da Sabha na kudancin Libya, ya tashi daga birnin Sabha zuwa birnin Lagos cibiyar kasuwancin Najeriya. Kaza lika a ranar Laraba, jirgi na biyu dauke da wasu 'yan ci ranin kasar Mali su 129, da suka hada da mata 23 da iyalai 19, ya tashi daga kasar ta Libya.
Kasar Libya dai ta yi kaurin suna a matsayin sansanin yada zango ga bakin hauren wasu sassan nahiyar Afirka dake fatan tsallakawa nahiyar turai ta tekun Bahar Rum.
IOM ta ce daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, adadin bakin haure da aka tsare tare da mayar da su Libya daga tekun Bahar Rum ya kai mutum 12,584, yayin da mutum 411 suka rasu, baya ga wasu 512 da suka bace bayan barin su gabar tekun Libya. (SAMINU ALHASSAN)