logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci a gudanar da hadin gwiwa wajen yaki da ta’addanci

2024-08-09 11:56:40 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su karfafa goyon baya, da hadin gwiwar yaki da ayyukan ta’addanci.

Geng, wanda ya yi kiran a jiya Alhamis, yayin zaman kwamitin tsaron MDD game da barazanar da ta’addanci ke yiwa zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, ya ce kungiyoyin ’yan ta’adda irin su Daesh, da Al-Qaeda da masu mara musu baya, na ci gaba da “Cin Karen Su BaBu Babbaka”.

Jami’in ya kuma yi gargadin cewa, yayin da sabon zagayen rikici tsakanin Falasdinawa da Isra’ila ke ci gaba da kazanta, mummunan tasirin hakan na kara bayyana, lamarin da ya haifar da karuwar muggan laifukan nuna kiyayya, da karuwar hadarin aukuwar hare-haren ta’addanci a kasashe da dama. A cewarsa wannan yanayi na da matukar tayar da hankali da haifar da damuwa.

Yayin da Geng Shuang ke bayyana muhimmancin hadin gwiwa a yaki da ’yan ta’adda, a hannu guda ya ce bai kamata yaki da ta’addanci ya zamo makamin fito na fito tsakanin manyan kasashen duniya ba, ko wata dama ta kafa kananan rukunonin adawar shiyyoyi, ko kafar tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashen duniya. (Saminu Alhassan)