logo

HAUSA

A rana ta 13 ta gasar Olympics dan wasan tsunduma cikin ruwa da 'yar wasan daga nauyi na Sin sun lashe lambobin zinari

2024-08-09 10:41:25 CMG Hausa

Shahararren dan wasan alkafura cikin ruwa na kasar Sin Xie Siyi, ya yi nasarar lashe lambar zinari a wasan tsunduma cikin ruwa daga tudun mita 3 ajin maza, a gasar Olympic dake gudana yanzu haka a birnin Paris, bayan ya samu maki sama da na takwaransa Wang Zongyuan.

Da wannan nasara, Xie Siyi ya ci gaba da rike kambin wasan, yayin da ita ma sabuwar hannu Luo Shifang daga Sin, ta lashe lambar zinari a gasar daga nauyi ajin 'yan wasa mata masu nauyin kilogiram 59.

Bayan kammala wasannin rana ta 13 a jiya Alhamis a gasar ta Olympic, Amurka ta yi gaba da yawan lambobin zinari 30, yayin da kasar Sin ke biye da guda 29.

Cikin wasannin da aka kammala a jiyan, a wasan tseren kwale-kwale na 'yan wasa biyu-biyu ajin maza na tazarar mita 500, 'yan wasan Sin Liu Hao da Ji Bowen, sun yi nasarar kammala tsere cikin minti guda da dakika 39.48, inda suka doke takwarorin su na Italiya Gabriele Casadei da Carlo Tacchini, wadanda suka kammala tseren cikin minti daya da dakika 41.08, suka kuma karbi lambar azurfa ta gasar.

A fannin wasan dambe kuwa, 'yar wasan kasar Sin Chang Yuan ce ta yi nasara kan takwararta ta kasar Turkiyya Hatice Akbas da maki 5 da nema. Da wannan nasara Chang ta lashe lambar zinari ta biyu da aka lashe a wasan dambe a daren jiya, inda ta karbi lambar zinari ajin 'yan wasan dambe mata masu nauyin kilogiram 54. (Saminu Alhassan)