logo

HAUSA

Kuri’un jin ra’ayi na CGTN: Masu bayyana ra’ayi sun zargi USADA da yin rufa rufa

2024-08-09 16:46:38 CMG Hausa

Batun rufa-rufa game da dan wasan tseren Amurka Erriyon Knighton da aka zarga da amfani da abubuwa masu kara kuzari yayin wasa, ya bankado zargin da ake yiwa hukumar yaki da amfani da abubuwan kara kuzari yayin wasanni ta Amurka wato USADA da boye gaskiya, da yin fuska biyu, da amfani da karfin iko ba bisa ka’ida ba.

Game da hakan, wasu kuri’un al’umma da kafar CGTN ta tattara sun nuna kaso 95.57 bisa dari na al’ummun da suka bayyana ra’ayoyinsu daga sassa daban daban na duniya, na zargin USADA da yiwuwar rufe gaskiya kan ’yan wasan Amurka, da aka tabbatar sun yi amfani da abubuwa masu kara kuzari.

A watan Maris da ya shude, hukumar yaki da amfani da abubuwa masu kara kuzari yayin wasanni ta kasa da kasa WADA, ta samu Erriyon Knighton da laifin amfani da abubuwan kara kuzari, amma duk da haka hukumar USADA ta kyale shi ya shiga wasu wasanni ba tare da la’akari da hukuncin WADA ba. Sai dai kawai USADA ta ce wai dan wasan ya ci wani nama ne gurbataccen wanda ya sanya aka same shi da wancan laifi.

Amma a daya bangaren WADA ta fitar da sanarwa, inda ta ce ba ta taba baiwa hukumar USADA ikon barin irin wadannan ’yan wasa da aka kama da lafin su shiga gasanni ba, domin hakan zai iya zubar da kimar gasanni. 

Game da hakan, sakamakon kuri’un jin ra’ayi na CGTN, sun nuna cewa kaso 90.15 na jama’ar da suka bayyana matsayar su na ganin Amurka ta rufe laifin Knighton, har ta ba shi damar shiga gasar Olympic ta birnin Paris, wanda hakan ya yi matukar gurgunta kima da makasudin gasanni. Har ila yau, kaso 96.54 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na ganin abun da Amurka ta yi misali ne na yin fuska biyu. Yayin da wani kason da ya kai 95.63 bisa dari ke ganin da yawa daga ‘yan wasan Amurka na gabatar da shaidun bogi na gwaje gwajen da aka yi musu.

Bugu da kari akwai kaso mai yawa da ya kai 96.23 bisa dari dake ganin ya dace a kara yawan gwajin da ake yiwa ’yan wasan Amurka masu halartar gasar Olympic ta Paris, domin dawo da kima da kwarin gwiwar adalci tsakanin sassan kasa da kasa kan gasar.

An gudanar da kuri’un jin ra’ayin al’ummar na CGTN ne ta harsunan Turanci da Faransanci, da Larabci, da harsunan Sifaniya da Rasha, inda masu bayyana ra’ayi 14,580 suka fayyace matsayarsu cikin sa’o’i 16.

(Saminu Alhassan)