Isra’ila ta amince da tsagaita bude wuta a zirin Gaza don tattaunawa
2024-08-09 10:57:42 CMG Hausa
Da sanyin safiyar Jumma’ar nan ne ofishin firaministan Isra’ila, ya ba da sanarwar cewa, bangaren Isra’ila ya amince da tsagaita bude wuta a zirin Gaza domin samun damar tattaunawa, kuma ya shirya tura tawagar wakilin tattaunawar ranar 15 ga watan nan.
Sanarwar ta ce, Isra’ila za ta tura tawagar wakilin tattaunawa zuwa wurin da za a tsara, da kuma tabbatar da matsayarta kan wasu kananan abubuwan dake cikin yarjejeniyar da za a gudanar.
Shugabannin Qatar, da Masar da na Amurka, sun bayyana a cikin wata sanarwar hadin gwiwa a daren jiya Alhamis cewa, shugabannin kasashen uku sun yi kira ga Isra’ila da Hamas da su amince a tattauna a birni Doha ko Alkahira a ranar 15 ga watan nan, da zummar warware dukkanin sabani dake tsakani, da kuma cimma yarjejeniya nan da nan.
Tun bayan barkewar rikicin Faladinu da Isra’ila a wannan sabon zagaye, Isra’ila da Hamas sun gudanar da tattaunawa sau da dama. To sai dai kuma baya ga cimma tsagaita bude wuta na dan lokaci, da kuma musayar sakin wasu da ake tsare da su a watan Nuwamban bara, ba a kara samun wani ci gaba ba. (Safiyah Ma)