DGPC: Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 77 a Nijar
2024-08-09 10:24:55 CMG Hausa
A jamhuriyar Nijar a yayin wani taron manema labarai, da ta kira a ranar jiya Alhamis 8 ga watan Augustan shekarar 2024 a birnin Yamai, babban ma’aikatar dake kula da fararen hula ta kasa DGPC ta bayyana cewa, ruwan sama da aka samu a yankunan kasar Nijar sun janyo asasar rayuka da asarar dukiyoyi.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
A cewar wannan sanarwa ta babban ma’aikatar da ke kula da kare fararen hulla DGPC, ambaliyar ruwa a kasar Nijar ta haddasa mutuwar mutane 77, daga cikinsu mutane 34 ta hanyar nutsewa yayin da mutane 43 cikin rugujewar gidaje, haka kuma an samu wadanda suka jikkata 85 da kuma mutane 75,711 da matsalar ta rutsa da su zuwa ranar 2 ga watan Augustan shekarar 2024.
Wannan ambaliyar ruwa, a cewar sanarwar ta shafi jihohi 42, kananan hukumomi 116 da kuma unguwanni gami da kauyuka 521. Haka kuma an samu asara a bangaren dabbobi na wajen 11,657, da kuma asarar abinci na ton 12,785 da kuma barnar kayayyaki da dama.
Babbar ma’aikatar kare fararen hula DGPC ta bayyana cewa, yankunan da matsalar ruwa ta shafa a kasar ta Nijar sun hada da yankin Maradi tare da mutuwar mutane 25, yankin Zinder tare da mutuwar mutane 18, sannan yankin Tahoua tare da mutuwar mutane 15, yankin Agadez da mutuwar mutum 9, yankin Dosso da mutuwar mutum 5, birnin Yamai tare da mutuwar mutum 3 sai kuma daga karshe yankin Diffa da ya yi rejistan mutuwar mutum 2.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.