logo

HAUSA

Dole ne bangaren Amurka ya mai da martani ga duniya game da amfani da maganin kara kuzari yayin wasanni

2024-08-09 11:27:45 CMG Hausa

 

A halin yanzu, an riga an kammala rabin gasar wasannin Olympics ta Paris ta shekarar 2024, amma a yayin gasar, kafofin watsa labarai da hukumomi na Amurka, suna ta maganganu marasa tushe, tare da yin Allah wadai da ’yan wasan sauran kasashe cewa wai suna shan maganin kara kuzari ba bisa ka’ida ba, amma a sa’i daya kuma, sun kare ’yan wasan kasarsu wadanda aka yiwa gwajin shan maganin kara kuzari a hukumance, wanda hakan ya nuna cewa, Amurka tana da “ka’idoji iri biyu”, ta kuma siyasantar da wasannin motsa jiki, da kuma amfani da su a matsayin makamai.

A ranar 7 ga watan nan, hukumar yaki da shan maganin kara kuzari yayin wasanni ta duniya wato WADA, ta ba da sanarwar cewa, tun daga shekarar 2011, a kalla akwai misalai guda uku, inda hukumar yaki da shan maganin kara kuzari yayin wasanni ta Amurka wato USADA, ta amince da ’yan wasan da suka yi amfani maganin Steroid da EPO, amma suka samu damar ci gaba da shiga gasa, a maimakon yi musu hukunci.

Sanarwar ta ce, hakan ya sabawa ka’idar WADA, wadda aka tsara don kare mutuncin gasar wasannin motsa jiki, ya kuma gurgunta adalcin gasar wasannin motsa jiki, da kuma yin barazana ga lafiyar 'yan wasan da abin ya shafa.

A sa’i daya kuma, bisa binciken intanet da CGTN na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya yi tsakanin wadanda aka bincika a duk fadin duniya, ya nuna kaso 95.01 cikin dari na wadanda aka bincika da zargin danyen aikin shan maganin kara kuzari a bangaren Amurka, yaki ne da ’yan adawar kasar bisa sunan wasannin motsa jiki, kana kaso 96.84 cikin dari sun yi imanin cewa, bangaren Amurka ya rasa mutunci a idon WADA, kuma kaso 96.11 cikin dari sun yi kira ga sassan kasa da kasa da su bi ruhin Olympics, su kiyaye mutunci, da adalci na hukumomin wasannin motsa jiki na kasa da kasa tare.

Wadannnan ra’ayoyin da shawarwarin sun tabbatar da mummunan aikin da Amurka ta yi a fannin kare amfani da maganin kara kuzari yayin wasannin motsa jiki, kaza lika hakan ya nuna cewa, kasashen duniya na kallon Amurka a matsayin wadda ke kare “babban matsayi” ta ko wane irin hali. (Safiyah Ma)