logo

HAUSA

Kocin wasan sarrafa jiki wato Acrobatics na Kenya: Haskaka rayuwata ta wasan Acrobatics a kasar Sin

2024-08-08 16:41:10 CMG Hausa

Kimanin shekaru 40 da suka wuce, Mathias Kavita, dan shekaru 12 da haihuwa a lokacin, ya zo kasar Sin, kuma ya koyi fasahar sarrafa jiki wato Acrobatics a kungiyar 'yan wasan Acrobatics dake birnin Guangzhou. Kawo yanzu, fasahar wasan Acrobatics daga kasar Sin mai nisa ta bazu zuwa Kenya dake gabashin Afirka, wadda ta shaida hadin gwiwar abokantaka da mu'amalar al'adu tsakanin kasashen biyu. A cikin shirinmu na yau, bari mu ji labarin wani kocin wasan sarrafa jiki wato Acrobatics dan asalin kasar Kenya mai suna  Mathias Kavita da kasar Sin.