An fara daukar matakan dakile yawan sare itatuwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya
2024-08-08 09:36:12 CMG Hausa
Hukumar raya yankin arewa maso gabashin Najeriya ta bukaci gwamnatocin dake shiyyar da su marawa kokarin da take yi wajen yaki da yawaitar sare itatuwa da jama’a ke yi domin yin girki da sauran bukatu.
Babba jami’in hukumar dake lura da jihar Gombe Alhaji Rufa’i Lawan ne ya bukaci hakan ranar Talata 6 ga wata a garin Gombe yayin taron yaye wasu matasan jihar da hukumar ta horas a kan hanyar dabarun samar da makamashin girki ta amfani da bawon Rake da buntun Shinkafa.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Alhaji Rufa’i Lawan ya ce, tun bayan samar da hukumar ta himmatu wajen bukatar gwamnatoci da su samar da hanyoyin da al’umominsu za su rinka amfani da shi a mastayin makamashin maimakon sare itatuwa barkatai wanda hakan ke haifar da matsaloli masu yawan gaske, inda ya ba da misali da tsananin zafin da aka yi a bana a akasarin jihohin dake shiyyar, wanda duk yana da nasaba da illlar sare itatuwa.
Ya ce shirin bayar da horo yana da manufar samarwa matasan yankin sana’o’in dogaro da kai.
Jami’in hukumar raya yankin arewa maso gabashin Najeriya mai lura da jihar Gombe, haka kuma ya ce, bayan an yaye matasan, hukumar ta samar musu da injinan sarrafa makamashin kyauta domin fara gudanar da wannan sana’a.
“Wannan shiri zai taimaka sosai saboda farko muna fama da matsala na zaizayar kasa, in ka lura abun da ake amfani da shi ana amfani da totuwar masara ko buntun shinkafa wanda dukkanninsu muna amfani da su yau da gobe, wanda kuma idan aka yi amfani da su zai zama ke nan mun samu sauyi daga itacen da ake amfani da su a gidaje, kuma wannan sabon tsarin da za a rinka amfani da shi ya fi rike zafi.”
Daya daga cikin matasan da suka samu horon ya yaba matuka bisa damar da aka ba su.
“Wannan abun da aka koya mana, in Allah ya yarda za mu je mu kara fadada shi mu koyawa kannenmu da abokanmu wadanda ba su zo nan wurin ba, inda za su tabbatar da ganin cewa wannan horo da aka koya mana bai tashi a banza ba.” (Garba Abdullahi Bagwai)