logo

HAUSA

Nijeriya ta gargadi kasashen waje game da tsoma baki cikin zanga-zangar tsadar rayuwa dake wakana a kasar

2024-08-08 09:47:36 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Nijeriya Yusuf Tuggar, ya yi kira ga kasashen duniya su guji tsoma baki cikin zanga-zangar tsadar rayuwa dake gudana a kasar, yana mai cewa, gwamnati na iya bakin kokarin magance matsalolin ‘yan kasar.

Yusuf Tuggar ya bayyana haka ne jiya Laraba, yayin wani taro da jami’an diplomasiyya dake Nijeriya, inda kuma ya nemi goyon baya daga kasa da kasa wajen magance kalubalen tattalin arziki da kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya dake ciki da wajen kasar.

Ya ce yayin da gwamnati take ci gaba da aiki tukuru ta hanyar aiwatar da gyare-gyare domin shawo kan kalubalen da Nijeriya da al’ummarta ke fuskanta, ta san cewa babu wata kasa da za ta lamunci a tsoma baki cikin harkokinta na gida. Ya kuma nanata cewa, kasar na tafiyar da harkokinta bisa doron doka kuma gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen kare jama’arta.

Bugu da kari, ministan ya ce gwamnati za ta dauki matakin da ya dace kan duk wani bako mazaunin Nijeriya da aka samu yana mara baya ga zanga-zangar ta kowacce hanya ko neman tsoma baki cikin harkokin kasar kai tsaye ko a fakaice. (Fa’iza Mustapha)