logo

HAUSA

Zheng ta kafa tarihin lashe lambar zinari a wasan tennis

2024-08-08 20:13:39 CMG Hausa

Yayin gasar Olympics ta birnin Paris dake gudana yanzu haka, sabbin fuskoki da dama sun bayyana, wadanda kuma suka kai ga wasannin karshe tare da lashe lambobin yabo a karon farko. A gasar kwallon tennis, irin wadannan ‘yan wasa maza da mata a baya sun taka rawar gani a gasanni daban daban na Grand Slam, amma ba su taba kaiwa ga lashe lambar zinari ta Olympic ba. Cikin irin wadannan ‘yan wasa akwai Dominika Cibulkova, da Kevin Anderson, da Mark Philippoussis, da Todd Martin, da Greg Rusedski, da Eugenie Bouchard da Mardy Fish.

‘Yar wasan tennis ta kasar Sin Zheng Qinwen na cikin wannan rukuni, domin kuwa watanni 7 kafin gasar ta Olympics ta yi rashin nasara a wasan karshe na gasar Australian Open, kafin ta kai ga cimma nasarar lashe zinari a Olympics din dake gudana yanzu haka.

Kafin zuwan ta gasar Paris, Zheng ta yi rashin nasara a hannun Aryna Sabalenka, da wata rashin nasarar a hannun Elina Avanesyan a gasar French Open cikin watan Mayu, kana ita ma Lulu Sun ta doke ta a gasar Wimbledon a cikin watan da ya gabata, wanda hakan ya sa da dama ke nuna damuwa game da makomar Zheng a gasar Paris. Amma duk da haka, a wannan wata na Agusta a gasar Olympics ta Paris, Zheng ta yi nasara a wasan karshe kan Roland Garros, tare da lashe lambar zinari a wannan babbar gasa ta kasa da kasa.

Lambar zinarin da Zheng ta lashe, tare da sauran tarin lambobin yabo da ‘yan wasan kasar Sin suka lashe kawo yanzu, sun nuna kwazo da jajircewar kaiwa ga cikakkiyar nasar, wanda hakan ke wakiltar cimma burin ta a wannan fage na wasan tennis, da ma burin ‘yan wasa mata daga Asiya da Sin a gasar tennis ta Olympic.

Lambar zinari da Zheng mai shekaru 21 ta lashe na iya zama mabudi na karin lambobin yabo da dama da za ta kai ga lashewa a nan gaba, ko kuma irinta ta karshe. Amma ko ma me ya faru nan gaba, tabbas wannan lamba ta zinari da Zheng ta lashe, za ta karfafa gwiwar ‘yan wasa maza da mata masu karancin shekaru daga inda ta fito, kuma lambar da ta lashe ba za ta zamo ta karshe ga irin wadannan matasan ‘yan wasa daga kasar Sin ba.

Cikin tsokacin da Zheng ta yi ga matasan ‘yan wasan tennis, da masu kallon wasan da suka tsaya har dare domin kallon wasannin da ta buga daga kasar Sin, ta ce "Ina son bayyanawa matasan ‘yan wasa cewa su zama masu jarunta da kokarin cimma burin su. Cimma buri na bukatar tsara burika, amma fa hanyar cimma nasarar hakan na tattare da kalubaloli, da jin kokwanto, da sadaukarwa. Dole mutum ya nishadantu da hanyar cimma nasara, saboda duk wata rashin nasara mataki ne zuwa ga babbar nasar. A inda nake yanzu a yau, ina iya cewa na gamsu da dukkanin kwazo na. Tun da ni ma matashiya ce, kuna iya samun darashi daga gare ni, kuma har kullum ina fatan zama daya daga masu zaburar da aniyar dukkanin yara, ta yadda za su kara nuna sha’awar su ga wasan tennis".

Duk da cewa yanzu ne Zheng ta fara haskakawa a harkar wasanni, tuni ta fahimci rawar da za ta iya takawa wajen karfafa gwiwar sauran yara masu tasowa, ba wai kawai ta fannin lashe lambobin yabo kadai ba, har ma da ingiza kuzarin sauran yara dake tafe.

Bayan kusan shekaru 10 da wata matashiyar daga kasar Sin mai suna Li Na, ta yi nasarar lashe lambar zinari a gasar tennis ta French Open, a yanzu ma masu sha’awar wasanin sun samu wata sabuwar tauraruwa da za su rika koyi da nasarar ta. Kuma duk da cewa gasar Olympic ba ta kai matsayin manyan gasannin tennis na kasa da kasa da ake gudanarwa ba, da yawa daga Sinawa masu sha’awar wasan, ciki har da mahaifin Zheng na ganin Olympic babbar gasa ce ta kololuwa.

Game da hakan, Zheng ta ce "Na san har kullum baba na yana daukar gasar Olympic da muhimmanci sama da sauran manyan gasannin kasa da kasa na tennis wato ‘Grand Slam’. Ina ganin dukkanin Sinawa masu sha’awar wasan ma haka ne ra’ayin su, har da ni kai na, kamar yadda ku ke gani. Tun ina da shekaru 10, baba na yake magana kan gasar ‘Grand Slam’ da Olympics. Na san gasar Olympics ta fi masa muhimmanci sama da ‘Grand Slam’. A shekarar 2022, na fada yayin wata zantawa da manema labarai cewa ina fatan zuwan Olympics na 2024. Amma duk da hakan na san ci-da-zuci kan haifar da rashin nasara. Wannan gasa ta Olympics ta jima a zuciya ta, ta saka min matsin lamba da damuwa. Ina ganin tamkar ina wakiltar daukacin kasar Sin ne a wasan tennis, musamman ganin yadda Sinawa ke ta nuna min goyon baya. Lashe lambar zinari ‘Kwalli ce ta biya kudin sabulu’ ”.