Kasar Sin ta fadada cibiyoyin kiyaye ikon mallakar fasaha zuwa 73 a fadin kasar
2024-08-08 20:21:16 CMG Hausa
Bayanan da hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta kasar Sin ko CNIPA ta fitar a yau Alhamis sun nuna cewa, adadin cibiyoyin kiyaye ikon mallakar fasahar da ake ginawa da kuma wadanda ke aiki a kasar Sin sun kai 73.
Hukumar ta ce, an rarraba wadannan cibiyoyin a larduna da jihohi masu cin gashin kansu da manyan biranen da ke karkshin shugabancin gwamnatin tsakiyar kasar guda 28, ciki har da guda biyu a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.
Kwanan nan ne dai hukumar ta CNIPA ta amince da gina wata cibiyar kiyaye ikon mallakar fasaha a Haikou, babban birnin Hainan, wadda a nan gaba za ta gudanar da aikin kiyaye ikon mallakar fasaha cikin sauri kuma bisa daidaito a fannonin masana'antar kera kayan aiki da masana'antar sinadarin magunguna wato biopharmaceutical.
Yadda Haikou ya janyo hankalin cibiyoyin bincike da manyan masana'antu, ya haifar da ci gabansa mai karfi, yayin da darajar kayayyaki da hidimomin da wadannan masana'antu biyu dake Haikou suka samar ta zarce dalar Amurka biliyan 5.6 a shekarar 2023. (Yahaya)