Binciken CGTN: Wadanda suka bayyana ra’ayinsu sun yi tir da danniyar da Amurka ke yi a fagen wasanni
2024-08-07 20:07:44 CMG Hausa
Amurka na kara zuzuta batun shan kwayoyin kara kuzari. Batancin da ta yi ya janyo karin suka daga kasashen duniya. A cewar wani binciken jin ra'ayin jama'a ta yanar gizo da kafar CGTN ta gudanar, kashi 95.01 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayinsu sun yi kakkausar suka ga Amurka kan danne abokan fafatawarta da sunan wasanni, suna sukar hakan da cewa, danniya mai salon Amurka ta keta ka’idojin wasannin Olympics.
Gwajin da aka yi wa dan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Amurka Erriyon Knighton ya nuna cewa, ya sha kwayar kara kuzari a watan Maris na wannan shekara. Amma hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta Amurka ba kawai kin dakatar da shi ta yi ba, har ma ta ba shi damar shiga gasar wasanni ta Paris, kuma kusan kashi 90 cikin 100 na 'yan wasan Amurka ba su bi ka'idojin hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta duniya ba.
A cikin binciken, kashi 96.25 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayinsu sun yi kakkausar suka ga Amurka game da nuna fuska biyu a cikin ka'idojin yaki da shan kwayoyin kara kuzari. Bugu da kari, Amurka ta yi barazana ga hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta duniya da abin da take kira "matsayin wakilcin da ya dace da gudummawar tattalin arzikinta" ta hanyar dakatar da taimakon kudi. A cikin binciken, kashi 95.01 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayinsu sun soki wannan furucin, wani nau’in danniya da tilastawa da Amurka take yi a fagen wasanni. Kashi 93.45 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayinsu sun ce, Amurka na kara siyasantar da batun shan kwayoyi masu kara kuzari da yin amfani da batun, a kokarin kara nuna karfi baya ga fagen siyasar kasa da kasa da diflomasiyya. (Yahaya)