logo

HAUSA

Hamas ta sanar da nadin Yahya Sinwar a matsayin sabon shugabanta

2024-08-07 10:27:37 CMG Hausa

Kungiyar Hamas ta sanar da nadin Yahya Sinwar a matsayin shugaban ofishinta na siyasa, domin ya maye gurbin marigayi Isma’il Haniyeh, wanda aka kashe a karshen makon da ya gabata. Kungiyar ta sanar da nadin ne a jiya Talata.

Yahya Sinwar mai shekaru 61, ya kasance shugaban Hamas a zirin Gaza tun daga shekarar 2017. Ya kuma shafe shekaru 20 a gidan yarin Isra’ila, inda aka sake shi a shekarar 2011 karkashin wata yarjejeniyar musayar fursunoni. Isra’ila na ganin shi a matsayin daya daga cikin wadanda suka kitsa harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoban bara. (Fa’iza Mustapha)