Sin ta kara samun lambobin yabo a rana ta 11 ta gasar Olympics na Paris
2024-08-07 13:45:54 CMG Hausa
A rana ta 11 ta gasar wasannin Olympics ta Paris, kasar Sin ta mamaye dandalin gasar nutso ta mita 10 ta mata, inda Quan Hongchan ta samu lambar zinari, yayin da ‘yar uwarta Chen Yuxi ta samu lambar azurfa. ‘Yar wasan kasar Sin Zhao Jie, ta samu lambar tagulla a matakin karshe na wasan jifa da mulmulallen dalma na mata, yayin da Yang Wenlu ta samu lambar azurfa a gasar dambe ta mata masu nauyin kg 60.
A sauran wasanni, Winfred Yavi ta Bahrain ta samu lambar zinari a matakin karshe na gasar tsere ta Steeplechase ta mita 3000, inda ta karya bajintar da Gulnara Samitova Galkina ta Rasha ta yi a wasannin Olympics na Beijing na 2008. ‘Yar wasan Uganda Peruth Chemutai ce ke bi mata baya da lambar azurfa, sai kuma Faith Cherotich ta kasar Kenya da ta zo na 3 da lambar tagulla.
A daya daga cikin wasanni mafiya ban sha’awa, Mijain Lobez na Cuba, ya kafa sabon tarihi kafin yin ritaya, inda ya lashe lambar zinari na 5 a jere a salon wasan kokawa na Greco-Roman, a wasannin Olympics. Lopez da aka fi sani da “El Terrible” ya kara kare lambunsa a matsayin daya daga cikin ‘yan wasan kokawa mafiya fice.
Bayan kammala gasannin Olympics a rana ta 11, Amurka ta kankane teburin lambobin yabo da lambobin zinari 24 da na azurfa 31 da tagulla 31, sai Sin dake bi mata baya da zinari 22 da azurfa 21 da tagulla 16. Yayin da Australia ke matsayi na 3 da zinari 14 da azurfa 12 da tagulla 9. (Fa’iza Mustapha)