logo

HAUSA

An samu karuwar mutanen da suka yi yawon bude ido a lokacin zafi a kasar Sin

2024-08-07 22:31:00 CMG Hausa

Adadin fasinjojin da suka yi yawon bude ido a kasar Sin, ya rika karuwa, tun daga ranar 1 ga watan Yulin shekarar da muke ciki, wato tun da aka shiga lokacin zafi a kasar. Kuma adadin fasinjojin da suke zirga-zirga a kowace rana a kasar, ya kai miliyan 170, adadin da ya karu da kaso 2.6 bisa dari idan aka kwatanta da na bara.