Hukumar shige da fice a Najeriya ta sha alwashin kamo masu iza wutar zanga-zanga a kasar da suke zaune a kasashen waje
2024-08-07 08:58:24 CMG Hausa
Hukumar lura da harkokin shige da fice ta tarayyar Najeriya ta sanar da cewa, yanzu haka ta sanya ido sosai a kan ’yan Najeriyar da suke zuga mutane wajen fitowa zanga–zanga alhalinsu, kuma suna zaune a kasashen ketare.
Shugabar hukumar Mrs Kemi Nandap ce ta tabbatar da hakan bayan kammala taron shugabannin hukumomin tsaro na kasa jiya Talata 6 ga wata a birnin Abuja. Ta ce, tuni aka kammala shirin kame irin wadannan mutane da zarar sun shigo Najeriya.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ko da yake dai shugabar hukumar shige da ficen ta kasa ba ta bayyana sunayen irin wadannan mutane ba, amma dai ta ce suna da cikakkun sunayensu a hannu, kuma da zarar an damke su ba za`a yi wata-wata ba wajen mika su ga hannun hukuma.
Mrs Kemi Nandap ta ci gaba da bayanin cewa, hukumar ta samar da jami’anta da dama a kan iyakoki na kasa da kuma filayen jiragen sama domin tabbatar da sanya ido sosai tun bayan fara zanga-zangar gama gari.
Haka kuma hukumar ta kara tsananta lura wajen ganin cewa kasashen duniya ba su sanya hannu ba a cikin zanga-zangar.
A yayin taron dai, daraktan janaral na hukumar tsaro na DSS Yasuf Magaji Bichi ya tabbatar da cewa, hukumar tasa ta gano tare da kulle asusun ajiyar mutanen da suke daukar nauyin zanga-zangar a Najeriya.
Alhaji Yusuf Bichi wanda ya smau wakilcin jami’in yada labaran hukumar Mr Peter Afunanya ya ce, da yawa daga cikin irin wadannan mutane suna zaune ne a kasashen waje kuma ma’aikatan hukumar na bibiyar su sannu a hankali. (Garba Abdullahi Bagwai)