logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su ba da tallafin magance rikicin jin kai a Sudan

2024-08-07 13:54:15 CMG Hausa

 

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya ce ba a taba ganin irin kalubalen jin kai da Sudan ke fuskanta ba a tarihi, inda ya ce kamata ya yi al’ummar duniya su kara ba da muhimmanci ga bayar da tallafi don cika alkawarin da ake yi na ba da taimako, ta yadda za a sassauta wannan matsala.

Dai Bing ya bayyana haka ne jiya Talata, a gun taron tattauna batun jin kai a kasar Sudan, wanda kwamitin sulhu na MDD ya gudanar.

A cewarsa, Sin na mai da hankali sosai kan halin jin kai a Sudan da wasu rahotannin da majalisar ta gabatar, musamman ma batun rashin hatsi. Ya ce daukar matakan da suka wajaba don sassauta rikicin jin kai da kasashen duniya ke yi kadai bai wadatar ba, ya kamata su kuma bayar da tallafi ga Sudan a fannin tabbatar da zaman rayuwa da raya tattalin arziki da sauransu, ta yadda za a taimakawa kasar daga karfinta da tabbatar da bunkasar tattalin arzikinta da kokarin rage illar da rikici zai yi wa harkokin tattalin arziki da zaman rayuwar jama’a. (Amina Xu)