logo

HAUSA

Har Yanzu A Wasu Sassan Kasar Sin Ana Ci Gaba Da Dakile Bala'in Ambaliyar Ruwa

2024-08-07 07:14:08 CMG Hausa

Tun da muka shigo lokacin daminan bana, yankuna daban-daban a fadin kasar Sin sun yi ta fama da ruwan sama kamar da bakin kwarya kuma na tsawon lokaci, lamarin da ya haifar da ambaliya ruwa a wasu yankunan. Hukumomin gwamnati masu kula da yanayin, da ruwa, da albarkatun kasa, da raya birane da karkara, sun ba da umarnin dakile ambaliya ga yankuna 18 da ake sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya. Haka ma kananan hukumomi suma sun ba da fifiko wajen lura da yanayin saukar ruwan sama da ambaliyar ruwa, tare da samar da tsare-tsare na gaggawa da kuma karfafa wuraren shawo kan ambaliyar ruwa. Ma'aikatar ba da agajin gaggawa ta kasar Sin a ranar Lahadin da ta gabata ta yi kira ga hukumomi da su kula saboda ana hasashen za a ci gaba da samun gagarumin ruwan sama a wasu yankuna nan da kwanaki masu zuwa. Hakan na nuni da cewa har yanzu ana ci gaba da aikin dakile bala’in ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar. 

A bisa ga binciken masana, dalilai guda uku ne suka haddasa ambaliyar ruwa a wannan shekara a yankin kudancin kasar Sin, na farko shi ne iska mai sanyi mai karfi kuma da ke tashi daga yankin arewa, yayin da tsohon iskar ya doshi kudu zuwa lardunan Guangdong da Jiangxi da yankin Guangxi Zhuang mai cin gashin kansa inda dumi da sanyi ke haduwa, shi yasa ake ci gaba da yin ruwan sama kamar da bakin kwarya, Dalili na biyu kuma shi ne yawan ruwan sama wanda ya sanya kasar ta kusa cika da ruwa wanda hakan ya sa ake samun ambaliya. Kuma dalili na uku shi ne matsanancin ruwan sama. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)