Nijar ta sanar da yanke huldar jakadanci da kasar Ukraine
2024-08-07 11:11:04 CMG Hausa
Gwamnatin mulkin soja ta Nijar, ta sanar da yanke huldar jakadanci da kasar Ukraine a jiya Talata.
Kakakin gwamnatin, Amadou Abdramane ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar.
Sanarwar ta kuma ruwaito kakakin ya yi Allah wadai da goyon bayan da Ukraine ke baiwa “kungiyoyin ta’addanci”, tare da fatan kwamitin sulhu na MDD zai yanke hukunci kan takalar da Ukraine ke yi.
Ko a ranar 4 ga wata, gwamnatin rikon kwarya ta kasar Mali ta fitar da sanarwa, inda ta bayyana cewa, a baya-bayan nan kasar Ukraine ta amince da shiga cikin hare-haren da kungiyoyin ’yan ta’adda masu dauke da makamai suka kaddamar, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da dukiyoyi ga sojojin Mali.
A watan Yulin wannan shekara, Nijar, Mali, da Burkina Faso suka sanar da kafa “Kungiyar Kawancen Kasashen Sahel”. (Bilkisu Xin)