logo

HAUSA

Firaministan Pakistan: Bunkasuwar Sin ya zama abin misali ga kasar

2024-08-07 14:13:27 CMG Hausa

 

Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya ce, cikakken zama karo na 3 na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya samu gaggarumar nasara, wanda ya bayyana hangen nesa da basirar shugaba Xi jinping.

Shehbaz Sharif ya bayyana haka ne yayin da ya yi hira da wakiliyar CMG dake kasar Pakistan a jiya Talata, ya kuma jinjinawa shawarar raya duniya bai daya da Xi Jinping ya gabatar. Ya ce, matakin ya zama wani babban buri na hadin kan kasa da kasa da shiyya-shiyya don samun bunkasuwa da wadata tare. Abin da ya alamanta cewa, Sin ita kadai ke samun bunkasuwa ba, tana kokarin taimakawa sauran kasashe masu tasowa, ta yadda za a tabbatar da wadatar dukkan bil Adama ta bai daya.

Kazalika, Sharif ya nanata ma’anar tsaro ga samun bunkasuwar kasa, ya ce, ba za a cimma burin samun bunkasuwa da wadata, inda babu tabbacin tsaro ba. A ganinsa, gaggauta maido da huldar diplomasiyyar Saudiyya da Iran da dai sauransu, sun kasance ainihin matakan da Sin ta dauka na tabbatar da shawarar da Xi Jinping ya gabatar, ana godiya sosai ga rawar a zo a gani da Sin take takawa na ciyar da huldar Saudiyya da Iran da ta koma hanya da ta dace.

A cikin zantawar, Sharif ya ce, Pakistan na tsayawa tsayin daka kan kare muradun Sin mai tushe kan batun Taiwan da Honkong da Xinjiang da tekun kudancin Sin da sauransu. A nata bangare, Sin kuma tana goyon bayan Pakistan da ta kare ikon mulkinta da ’yancin al’ummar da cikakken yankunanta. Lamarin dake bayyana dankon zumuncinsu da kyakkyawar huldar abota ta makwabta. (Amina Xu)