Najeriya za ta janye damar kin biyan haraji ga kayayyakin abinci da ake shigowa da su zuwa karshen watan Nuwamba
2024-08-06 10:33:21 CMG Hausa
Ministan harkokin noma da bunkasa samar da abinci a tarayyar Najeriya Sanata Abubakar Kyari ya ce, ’yan kasuwa za su ci gaba da cin gajiyar shirin gwamnati na shigowa da kayan abinci kasar ba tare da biyan haraji ba har zuwa karshen watan Nuwamban 2024.
Ya bayyana hakan ne a karshen mako lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Abuja. Ya ce, gwamnati na hasashen samun yalwar abinci bayan girbin hatsi a damunan bana a tsakanin watan Oktoba zuwa Nuwamba.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Sanata Abubakar Kyari ya ce, daman dai matakin da gwamnati ta dauka na wucin gadi ne domin dai dakile ci gaba da hauhawar farashin kayan abinci a kasa.
Ministan gona ya ci gaba da bayanin cewa an kiyasta cewa za a rinka shigo da tan dubu dari 3 zuwa dari 4 na nau’ika 5 na abinci da aka tsara shigowa da su a duk wata, wanda zai kai har zuwa watannin Oktoba zuwa Nuwamban wannan shekara. Ya ce, tun da farko gwamnatin tarayyar ta yanke shawarar baiwa ’yan kasuwa wannan dama ce saboda ’yan matsalolin da ake fuskanta a bangaren noman abinci, ko da yake ministn ya ce, ba gwamnatin tarayyar ce kadai take da alhakin warware matsalolin da sha’anin noma ke fuskanta ba.
“Hakika dai ma`aikatar gona ta tarayyar ta yarda tana da alhakin abubuwan da suke faruwa ta fuskar koma bayan da ake smau a fagen noman abinci, amma duk da haka su ma fa jihohi suna da ma’aikatun gona haka suma kananan hukumomi suna da sashen gona kaga ke nan dukkan matakan gwamnati uku suna da alhaki a kan jerin kalubale da bangaren noma a Najeriya ke fuskanta.”
Ya ce, wajibi ne a karfafa gwiwar manoma tun daga tushe ta wajen samar masu da tallafi da kayan aiki na zamani tare kuma da kyautata tsarin samar masu da rance mara ruwa ta yadda zasu mayar da hankali kan wadata kasa da abinici. (Garba Abdullahi Bagwai)