MDD ta zargi wasu jami’an UNRWA da hannu a harin da aka kaiwa Isra’ila a Oktoban bara
2024-08-06 10:47:26 CMG Hausa
Ofishin MDD mai sa ido kan ayyukan dake gudana a sassan kasa da kasa ko OIOS, ya ce akwai shaidu dake nuna yiwuwar sa hannun wasu jami’an samar da agaji na MDD, da na hukumar gudanar da ayyukan jin kai ga Falasdinawa ‘yan gudun hijira ta majalissar ko UNRWA, a harin da aka kaiwa kasar Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023.
Mataimakin kakakin babban magatakardar MDD Farhan Haq ne ya bayyana hakan a jiya Litinin yayin taron manema labarai da ya gudana, inda ya ce ofishin OIOS ya kammala bincike kan jami’an UNRWA su 19, da wasu jami’an dake aiki kai tsaye a sansanin a madadin UNRWA, an kuma yanke hukuncin dakatar da su daga aiki saboda kare martabar hukumar. (Saminu Alhassan)