logo

HAUSA

Kasar Sin za ta gina sabon tsarin samar da wutar lantarki

2024-08-06 20:49:01 CMG Hausa

Kasar Sin ta kaddamar da wani shiri na gina sabon tsarin samar da wutar lantarki a wani bangare na kokarin da kasar ke yi na neman bunkasuwa a fannin kiyaye muhalli da tabbatar da wadatar makamashi a yau Talata.

Shirin wanda hukumar kula da ayyukan yin gyare-gyare a gida da raya kasar Sin da hukumar kula da makamashi ta kasar da kuma hukumar kula da bayanai ta kasar suka fitar tare, ya bayyana matakan da za a dauka a fannoni tara tsakanin shekarar 2024 zuwa ta 2027.

Gwamnatin kasar Sin za ta yi kokarin kara samar da wutar lantarki mai tsafta, da inganta tashoshin samar da wutar lantarki daga kwal, da kuma fadada wuraren cajin motocin lantarki.

Har ila yau, shirin ya bayyana matakan da za a dauka na tabbatar da daidaiton tsarin samar da wutar lantarki na kasar Sin, da kara bunkasa hanyoyin rarraba wutar lantarki. (Yahaya)