Sin da Switzerland sun yi musayar ra’ayi kan batun Falasdinu
2024-08-06 20:57:55 CMG Hausa
Zhai Jun, wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin kan batun Gabas ta Tsakiya, ya gana da Wolfgang Amadeus Brulhart, wakilin kasar Switzerland a yankin Gabas ta Tsakiya a ranar Litinin ta wayar tarho.
Da yake gabatar da batun tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin Falasdinu 14 da aka gudanar a Beijing a watan Yulin bana, Zhai ya ce, kasar Sin tana matukar fatan bangarori daban daban na Falasdinawa za su tabbatar da hadin kan kasa da kafa kasa mai cin gashin kai tun da wuri bisa yin sulhu a cikin gida.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta yaba da kokarin da kasar Switzerland ke yi na aiwatar da shawarwarin kafa kasashe biyu, kuma a shirye take ta yi aiki da kasar Switzerland don ci gaba da ba da kyakkyawar gudummawa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Da yake taya kasar Sin murnar nasarar shiga tsakani a tattaunawar sulhun da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar Beijing, Brulhart ya ce, Switzerland tana kan matsayi daya da kasar Sin dangane da batun yin sulhu tsakanin bangarorin Falasdinu. Bangarorin Falasdinawa daban daban da suke kan matsaya guda tare da yin magana da murya daya, su ne abubuwan da ake bukata don cimma nasarar kafa kasashe biyu, da warware batun Falasdinu, a cewar Brulhart, inda ya yi kira da a ci gaba da tuntubar juna da kasar Sin kan wannan batu. (Yahaya)