logo

HAUSA

Sin ta zama ja gaba a teburin lambar yabo ta zinari

2024-08-06 10:19:02 CMG Hausa

‘Yan wasan kasar Sin sun lashe lambobin yabo da dama a rana ta 10 ta wasannin Olympics na Paris, inda tawagar kasar ta sake yi wa Amurka fintinkau a yawan lambobin zinari.

A ranar Litinin, tawagar kasar Sin ta samu lambobin zinari biyu, wanda ya kawo jimlar adadinsu zuwa 21.

Li Yuehong na kasar Sin ya fara da kafar dama a jiyan, inda ya lashe lambar zinari a gasar harbi da karamin bindiga daga tazarar mita 25.

A fagen wasanni sarrafa jiki kuwa, dan wasan kasar Sin Zou Jingyuan, ya yi nasarar samun maki 16.2 a gasar tsallen sarrafa jiki kan karafuna ta Parallel Bars, lamarin da ya sanya shi gaban dan wasan Ukraine Illia Kovtun da ya samu lambar azurfa. (Fa’iza Mustapha)