Kungiyar CEDEAO ta yi allawadai da kazaman hare-haren da aka kaiwa sojojin Mali a Tin-Zaouatine
2024-08-06 09:58:32 CMG Hausa
A cikin wata sanarwar yin allawadai da ta fitar a ranar jiya Litinin 5 ga watan Augustan shekarar 2024, kungiyar ci gaban tattalin arzikin yammacin Afrika ta CEDEAO ko ECOWAS, ta nuna damuwarta matuka kan matsalar tsaro a kasar Mali, bayan harin Tin-Zaouatine.
Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
A cewar wannan sanarwa, kungiyar CEDEAO ko ECOWAS na bibiyar halin da ake ciki da nuna damuwa kan matsalar tsaro a kasar Mali, tare da yin allawadai da babbar murya kan hare-haren baya bayan nan kan jami’an tsaron FDS na kasar Mali a kauyen Tin-Zaouatine dake arewacin kasar Mali kusa da iyaka da kasar Aljeriya, hare-haren ta’addancin da suka yi sanadiyyar mutuwar sojojin Mali da dama.
Ta hanyar wannan sanarwa, kwamitin kungiyar CEDEAO ko ECOWAS na isar da sakon ta’aziya ga gwamnatin Mali da al’ummar jamhuriyar Mali, da kuma iyalan mamatan.
Kwamitin kungiyar CEDEAO ya yi amfani da wannan dama, domin bayyana kin amincewa tare da yin allawadai da babbar murya da duk wani shisshigi na kasashen waje a shiyyar yammacin Afrika, da zai iya kasancewar barazana ga zaman lafiya da tsaro a wannan shiyya, tare kuma da nuna adawa kan duk wani shirin da zai tura shiyyar cikin tashin hankali da yake-yake na siyasar duniya.
A karshe, kungiyar CEDEAO ta jadadda niyyarta da kasancewa a shirye ga duk wani yunkurin da taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro a shiyyar yammacin Afrika, in ji wannan sanarwa. (Mamane Ada)