Mohamed Ibn Chambas ya yi kira ga Nijar da Benin da su mai da sabaninsu gefe domin bude iyakokinsu
2024-08-05 09:32:12 CMG Hausa
Shugaban Task Force kan fasalin ba da damar musanya na CEDEAO, dokta Mohamed Ibn Chambas ya yaba da kokarin baya bayan nan na kasashen Benin da Nijar kan neman daidaita shige de ficen mutane da kayayyakinsu da aka tsaida tun cikin watan Yulin shekarar 2023.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
A cikin wata sanarwar ta kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta CEDEAO ko ECOWAS mai magana da yawun rundunar Task Force, Mohamed Ibn Chambas ya yi kira ga shugabannin kasashen Nijar da Benin a wannan mako tun daga birnin Abujan Najeriya, tare da bayyana jinjina ga yunkurin tsoffin shugabannin kasar Benin biyu Nicephore Soglo da Thomas Boni Yayi, inda kuma a cikin sakon kuma tare da yin kira ga kasashen Benin da Nijar da su dauki alkawarin tabbatar da shige da fice na al’umma da kayayyaki a kasashe biyu.
Wannan kira ya biyo bayan ganin shige da fice na mutane da dukiyoyinsu a tsawon hanyar Cotonou-Niamey ya zama wata matsala tun yau da dan lokaci. Alhalin burin kafa wannan Task Force shi ne tabbatar da shige de ficen kayayyaki a yankin CEDEAO.
Haka kuma cikin sanarwar, an tunatar da cewa a yayin ziyarar masu shiga tsakani na tsoffin shugabannin kasar Benin a birnin Niamey, shugaban kasar Nijar Abdourhamane Tiani ya gana da wannan tawaga a hukunce.
A yayin wannan tattaunawa, bangarorin biyu sun yi musanya mai zurfi kan hanyoyi fita daga wannan rikici tsakanin Benin da Nijar, da tarihi ya gama, wannan kuma ya taimaka wajen aika manyan jami’ai a kasar Benin a karkashin jagorancin ministan cikin gida Mohamed Toumba zuwa kasar Benin domin tattauna hanyoyin fita daga wannan rikici.
Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.