Shugaba Tinubu ya yi kira ga ’yan Najeriya da su dauki darasi a kan asarar da ake yi yanzu
2024-08-05 09:31:04 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya ya ce, yana kwana da takaici a kan yadda ake samun asarar rayuka da kaddarori a sakamakon zanga-zangar da yanzu haka ake yi a duk fadin kasar.
Ya bayyana hakan ne jiya Lahadi 4 ga wata yayin jawabin da ya yi wa al’ummar kasar ta kafofin yada labarai. Ya ce, ya zama wajibi ya mika sakon jajensa ga wadanda zanga-zangar ta yi sanadin rayukansu da kuma wadanda suka tafka asarar kaddarori ciki har da gwamnati, inda ya ce, dole ne gwamnati da al’umma su hada hannu domin dakile ci gaba da faruwar hakan.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahato.
Bukatar neman masu zanga-zangar su janye daga kan tituna domin dai bayar da damar zaman sulhu da gwamnati yana daga cikin muhimman batutuwa guda 6 da jawabin shugaban kasar ya kunsa.
Sauran batutuwan sun hada da sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin take yi wadanda suka kunshi janye tallafin man fetur, wanda kamar yadda shugaban ya fada, yana daya daga cikin matakai masu tsauri da yake damun al’ummar kasa, amma dai gwamnati ta yi hakan ne da kyakkyawar manufa.
Ta fuskar ilimi da matasa kuwa wadanda kamar yadda ya fada su ne suka fi yawa a cikin jerin gwanon masu zanga-zangar, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa ta kirkiro da shirin bayar da rancen karatu ga dalibai tare kuma da samar da tsari na amfani da iskar gas ga ababen hawa domin saukaka sha’aini sufuri ga dalibai da kuma sauran al’umma.
Shugaban ya kuma yi magana a kan samar da ababen more rayuwa ga ’yan Najeriya inda ya ce, gwamnatinsa ta saka jari mai tarin yawa a bangaren sufurin jiragen kasa, gina tituna da habaka sha’anin wutar lantarki.
Yayin da a bangaren tsaro kuma, shugaban Bola Tinubu ya yi alkawarin cewa zai ci gaba da bijiro da hanyoyi daban daban da za su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, inda ya ce, tuni aka baiwa hukumomin tsaron kwarin gwiwa wajen tabbatar da hakan.
Shugaban ya kuma kara kira ga ’yan Najeriya, “Kasancewar yanzu haka mun shafe shekaru 25 muna kan tafarkin demokradiyya, kada ku sake makiya demokradiyya su yi amfani da ku wajen bijiro da wasu manufofi da ko kadan ba sa cikin doka, wadanda kuma tabbas za su iya mayar da hannun agogo baya a tafiyar da muke yi cikin salama kan tafarkin demokradiyya.” (Garba Abdullahi Bagwai)